OYA Magazine

Outstanding Young Achiever's Magazine

Abun takaici: Malamar asibiti ta siyar da yaro dan shekara 5 ga wasu ma’aurata a kan N15,000 a jihar Kano

Hukumar yan sanda na jihar Kano ta kama ma'aurata tare malamar asibiti masu cinikin yara

Majiya yace an kama masu laifin 10 ga watan octoba bayan barazanar da wata Hajiya Fatima tayi na siyar da jaririnta wanda yayi yayi sanadiyar kama su

Hukumar yan sanda na jihar Kano ta kama wasu ma’aurata tare sa wata malamar asibiti bisa laifin cinikin siyan yaro mai shekaru 5 a duniya.

Kakakin hukumar na jihar DSP Magaji Majiya ya bayyana haka ma manema labarai ranar laraba a garin kano.

Majiya yace an kama masu laifin 10 ga watan octoba bayan barazanar da wata Hajiya Fatima tayi na siyar da jaririnta wanda yayi yayi sanadiyar kama su.

“Mun samu labari daga Hajiya Fatima cewa wasu mutane na son siyan yaron ta. Shine muka gaya mata ta amince da cinkin siyar da yaron.

“Masu laifin sun siya yaron a kan N15,000 amma sun fara biyan N13,000” yace.

Kakakin yace sun kama daya daga cikin masu laifin mai suna Itopam Pious wanda ke iƙirari cewa ita malamar asibiti ne a asibitin ido na ECWA dake nan Kano yayin da take neman daukan yaron daga mahaifiyar sa.

A bisa bayanin sa malamar zata siya yaron ma wasu ma’aurata Mista da Misis Charles Bob-Manuel wanda suka yi balaguro daga jihar Ribas zuwa jihar Kano domin amsan rainon yaro bayan sun kwashi shekara 12 da yin aure kuma basu samu yaro.

Ya kara da cewa malamar asibiti ta amsa laifin amma ma’auratan sun musanta kansu da laifin.

A karshe Majiya yace har yanzu suna bincike kuma za’a gabatar dasu gaban kotu domin a yanke masu hukunci.

Source: pulse.ng
Link: Abun takaici: Malamar asibiti ta siyar da yaro dan shekara 5 ga wasu ma’aurata a kan N15,000 a jihar Kano

Comments

comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *