OYA Magazine

Outstanding Young Achiever's Magazine

Bisa ga rahoton da ya fitar: An sallami wakilin gidan rediyo na Freedom fm daga jerin yan jaridar gidan gwamnatin jihar Kano

Wakilin freedom fm da aka sallama

Wannan sallamar tana da alaka da labarin da wakilin ya fitar a baya na arangamar da gwamnan jihar yayi da yan fashi da makami a hanyar sa na zuwa garin Jos daga Abuja

Gwamnatin jihar Kano ta sallami wakilin gidan rediyon Freedom fm Abbass Yusha’u daga cikin yan jarida dake kawo rahoton gidan gwamnati.

Wannan sallamar tana da alaka da labarin da wakilin ya fitar a baya na arangamar da gwamnan jihar yayi da yan fashi da makami a hanyar sa na zuwa garin Jos daga Abuja.

A baya dai wakili daga ofishin yada labarai na gwamnatin ya tabbatar da labarin amma daga baya gwamnatin ta musanta haka.

Bayan aikawan da tayi ga gidan rediyon freedom fm na janye Abbas gwamnatin ta samu wani da zai maye gurbin sa.

Source: pulse.ng
Link: Bisa ga rahoton da ya fitar: An sallami wakilin gidan rediyo na Freedom fm daga jerin yan jaridar gidan gwamnatin jihar Kano

Comments

comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *